Fadar shugaban ƙasa ta ƙaryata wani zargi da ake wa shugaban ƙasa Muhammad Buhari kan cewa shugaban na ƙin jinin Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Tinubu a matsayin wanda zai gaje shi.
Mai magana da yawu shugaban kasan, Garba Shehu ya bayyana hakan a matsayin labarin ƙanzon kurege da kuma ake alaƙantawa da shugaban.
Don haka, Garba Shehu ya bayyana cewa fadar shugaban ƙasa a shirye take wajen miƙa shugabanci ga sabuwar gwamnati kuma tuni shirye-shiryen hakan sun yi nisa.
A kuma tabbatar da cewa mambobin kwamitin miƙa mulkin ya ƙunshi mutane daga ɓangarori biyu na gwamnati da kuma na sabuwar gwamnati.
Don haka, bai ga wani dalili da zai sa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙi sabon shugaban ƙasar ba wanda suka daɗe tare a fagen siyasa da shugabanci.
A ƙarshe Garba Shehu ya tabbatar da cewa shugaba Buhari ba shi da wani buri da ya wuce miƙa mulki da kuma komawa garinsu na Daura wanda shi ne burin kowanne shugaba mai barin gado.