Home » Shugaba Buhari Ya Shawarci Tinubu Kan Ƙara Wa Ma’aikata Albashi

Shugaba Buhari Ya Shawarci Tinubu Kan Ƙara Wa Ma’aikata Albashi

by Anas Dansalma
0 comment

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari mai barin gado ta bai wa zababben shugaban kasa Bola Tinubu shawarar kara wa ma’aikata albashi saboda shirin gwamnati na janye tallafin man fetur a watan Yuni mai zuwa.

Ministan kwadago na kasar Chris Ngige ne ya sanar da haka, inda ya ce tuni dama gwamnati mai barin gado ta kammala shirya yadda za ta kara wa ma’aikata albashi domin rage radadin janye tallafin man fetur din.

Sai dai duk da cewa bai zama wajibi gwamnatin Tinubu ta yi aiki da wannan shawara ba, amma matakin ya kara dora mata matsin lamba kan cika alkawarin yakin neman zaben da Tinubu ya yi cewa zai janye tallafin man fetur — duk kuwa da cewa gwamnatin Shugaba Buhari ta gaza janye shi saboda adawar da ‘yan kasa ke nunawa.

Tun da farko dai zababben shugaba Tinubu ya sha alwashin karkatar da kudaden tallafin man fetur din zuwa ga ayyukan bunkasa walwalar ‘yan kasa da gyaran tititunan da suka lalace gami da inganta ilimi da kiwon lafiya, amma bai ayyana batun karin albashi ba kamar yadda gwamnatin Buhari yanzu ke bayar da shawara.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?