Home » Gwamnatin Tarayya Za Ta Samar da Intanet Kyauta Ga ‘Yan Najeriya

Gwamnatin Tarayya Za Ta Samar da Intanet Kyauta Ga ‘Yan Najeriya

by Anas Dansalma
0 comment

A jiya ne Majalisar Zartarwa ta Tarayya FEC, ta amince da kashe Naira biliyan N24.20 a wasu kwangiloli biyu domin samar da intanet kyauta a wuraren taruwar jama’a 75 da suka hada da filayen tashi da saukar jiragen sama guda, manyan makarantu da kasuwanni guda 20 a fadin kasar nan domin tallafa wa kanana da matsakaitan masana’antu.

Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Isa Ali Pantami, ya ce hukumar sadarwa ta Ƙasa ce za ta gudanar da ayyukan.

Ya ce an zabo wurare mafiya karanci Uku daga cikin shiyyoyi shida da muke da su a siyasa.

Ya ce, A Kudu maso Yamma, akwai Jihar Legas da Ondo; a Kudu maso Gabas, Akwai jihar Imo, Anambra da Enugu; Kudu maso Kudu, akwai jihar Fatakwal da Akwa Ibom; a Arewa ta Tsakiya, Akwai Abuja da birnin Ilorin; a Arewa maso Yamma, akwai Jihar Kano, Sokoto da Kebbi; a Arewa maso Gabas, akwai birnin Yola, Maiduguri da Gombe.

Ya ce za a kammala aikin cikin ƙanƙanin lokaci, watanni hudu, mafi tsawo watanni biyar kuma akwai tanadin kudaden da ake bukata.

Pantami ya ce gwamnati mai ci ce ta tara kudaden da za a gudanar da ayyukan da su.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?