Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cire sunan Maryam Shetty a matsayin wadda za a naɗa kan muƙamin minista, inda ya maye ta da sunayen mutum biyu.
Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ne ya sanar da haka a wata wasiƙa da shugaban ƙasar ya aika wa majalisar kuma ya karanta yayin wani zama a yau.
Sunayen mutum biyu da Shugaba Bola Tinubu ya aika wa majalisar sun haɗar da Festus Keyamo da kuma Dr. Mariya Mairiga.
Ba a dai bayyana dalilin janye sunan Maryam Shetty a jerin ministocin da Tinubun zai naɗa ba