Home » Shugaba Tinubu ya aike wa majalisar Dattawa shirinsa na tura sojojin Najeriya Nijar

Shugaba Tinubu ya aike wa majalisar Dattawa shirinsa na tura sojojin Najeriya Nijar

by Anas Dansalma
0 comment
Shugaba Tinubu ya aike wa majalisar Dattawa shirinsa na tura sojojin Najeriya Nijar

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ya aike wa da majalisar Dattawa game da da shirin Kungiyar Raya Tattalin Arziƙi, ECOWAS, na aike wa da sojojinta kasar Nijar domin kawar da hafsoshin  sojin da suka yi juyin mulki a kasar.

Shugaban Majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ne ya bayyana hakan a yayin da yake karanta wasiƙar ga ‘yan majalisun ƙasar nan.

A cikin saƙon da shugaban ƙasar ya aike wa majalisar, ya ce sam ba ya goyon bayan juyin mulkin da aka yi a Nijar.

Ya kuma ce tuni Najeriya ta fara ɗaukar mataki na jan kunne a kan hafsoshin sojin ƙasar ta Nijar da suka haɗa da:

Sanya ido akan kowanne shige da fice a iyakin Najeriya da Nijar da katse wa Nijar wutar lantarki da dakatar da harkar kasuwanci da zirga-zirgar jirage sama masu fita ko shiga ƙasar ta Nijar.

Sauran matakan da shugaba Tinubu ya ɗauka sun haɗa da rufe duk wata hanya da za a iya amfani da ita wajen shigar da kaya musamman daga jihar Lagos da kuma wayar da kan al’umma kan manufar Najeriya na tabbatar da dimokraɗiyya.

Sannan akwai shirye-shirye na amfani da ƙarfin soji idan hafsoshin sojin Nijar ɗin suka cigaba da watsi da kiraye-kirayen ƙungiyar ECOWAS.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi