Home » ‘Yan majalisar tarayya sun mai da martani game da yin sama da fadi da biliyan 70

‘Yan majalisar tarayya sun mai da martani game da yin sama da fadi da biliyan 70

by Anas Dansalma
0 comment
'Yan majalisar tarayya sun mai da martani game da yin sama da fadi da biliyan 70

Ƴan Majalisar wakilan Najeriya sun fara mayar da martani dangane da sukar da ake musu ta warewa kansu Naira biliyan 70 daga cikin Naira biliyan 500 da suka amince wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kashe, wajen ba wa ‘yan kasar tallafin rage radadin janye tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi.

Da dama daga cikin ‘yan Najeriyar na ganin matakin da ƴan majalisar suka dauka ya nuna yadda suka fi fifita bukatunsu a kan na jama’a, wadanda dama ke cikin wahala.

Sai dai a cewar wasu daga cikin ‘yan Majalisar irin su Injiniya Sani Bala Tsanyawa daga Kano, sabanin yadda mutane ke cewar su za a raba wa kuɗin, za a yi amfani da su ne wajen yin gyare-gyare a majalisar, da biyan albashin ma’aikata masu musu hidima, da sauran bangarorin majalisar.

Sani Bala Ya yi bayanin cewa Naira biliyan 70 din da suka ware wa kansu na cikin wata Naira biliyan 300 da Shugaba Tinubu ya nema ne tun da farko, ba wai cikin biliyan 500 din da aka kebe domin rage wa talakawan kasar radadin janye tallafin mai ba.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi