Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta samu ci gaba sosai wajen magance matsalar rashin tsaro a faɗin ƙasar cikin shekaru biyu da suka gabata.
Shugaban ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na daƙile ayyukan ta’addanci da kuma tabbatar da zaman lafiyar ƙasa.
A wata sanarwa da Tinubu ya fitar a shafinsa na sada zumunta, a ranar Juma’a, ya ce ƙalubalen tsaro a Najeriya, da suka haɗa da ta’addanci da aikata laifuka, ana magance su da sabbin tsari da sauye-sauyen dabarun dawo da zaman lafiya a faɗin ƙasar.
“Haƙiƙa muna fuskantar ta’addanci – ƙalubalen da Najeriya ta fuskanta kusan shekaru ashirin, kuma ba za mu ja da baya ba, za mu yi nasara a kan ta’addanci kuma mu yi iƙirarin samun nasara a wannan yaƙin, ba za mu taɓa yin sulhu harkar tsaro ba.
“Najeriya ƙasa ɗaya ce mai haɗin kai, mun tashi tare, mun ci gaba tare, kuma mun ƙi yanke ƙauna domin tabbatar da ƙuduri.
- Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi a Aso Rock
- Za A Yi Babban Taron Tattauna Hanyoyin Magance Matsalar Tsaro A Arewacin Nijeriya
“Aikin da ke gabanmu yana da yawa, amma duk da haka ƙudurinmu ya fi girma, za mu ci gaba da ɗorewa tare da inganta nasarorin da muka samu na sake fasalin ƙasa da kuma samar da ci gaba a Najeriya.
“Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba kuma ba za mu bar wani abu ba a cikin aikinmu na kawar da masu aikata laifuka a cikin al’ummarmu, muna kira ga abokan haɗin gwiwarmu da su tsaya tsayin daka tare da mu yayin da muke ƙara faɗaɗa yaƙin da muke yi da ta’addanci, mun samu gagarumin ci gaba a cikin shekaru biyu da suka gabata, kuma za mu kawar da wannan barazana.”
