• Home  
  • Za A Yi Babban Taron Tattauna Hanyoyin Magance Matsalar Tsaro A Arewacin Nijeriya
- Babban Labari - Labarai

Za A Yi Babban Taron Tattauna Hanyoyin Magance Matsalar Tsaro A Arewacin Nijeriya

An shirya gudanar da babban taron tsaro a jihar Kebbi, a ranar Litinin mai zuwa 10 ga Nuwambar wannan shekara, domin tattauna hanyoyin magance karuwar matsalar tsaro a Arewacin Nijeriya. Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III zai jagoranci taron tare da tsohon hafsan hafsoshin soji kuma tsohon ministan cikin gida, Laftanar Janar […]

An shirya gudanar da babban taron tsaro a jihar Kebbi, a ranar Litinin mai zuwa 10 ga Nuwambar wannan shekara, domin tattauna hanyoyin magance karuwar matsalar tsaro a Arewacin Nijeriya.

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III zai jagoranci taron tare da tsohon hafsan hafsoshin soji kuma tsohon ministan cikin gida, Laftanar Janar Abdulrahman Bello Dambazau mai ritaya tare da halartar gwamnonin Arewa da masana tsaro da sauran manyan jami’ai.

Ana sa ran taron zai samar da dandalin tattaunawa da hadin kai domin dawo da zaman lafiya da karfafa hadin kan kasa.

Taron dai zai hada masu tsara manufofi, jami’an tsaro da kungiyoyin samar da ci-gaban al’umma da ‘yan jarida domin tsara dabarun sadarwa da za su taimaka wajen samar da yardar jama’a da hana tsattsauran ra’ayi da tallafa wa gyaran tsarin tsaro na Nijeriya.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai