Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya fara wani hutun kwana 10 daga yau Alhamis, inda yake sa ran yin kwanaki a ƙasashen Turai irin su Faransa da Birtaniya.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wani bayani da mai magana da yawo shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar a yau Alhmais.
Sanarwar ta ce “Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja yau, 4 ga watan Satumba domin fara hutu a Turai, a matsayin wani bangare na hutunsa na aiki na shekara ta 2025.
“Hutun zai ɗauki tsawon kwana 10.
“Shugaban kasar zai kwashe wani lokaci tsakanin Faransa da Birtaniya kafin ya koma ƙasar.”