Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya musanta iƙirarin da Femi Kuti ya yi a kansa, wanda ya ce Hukumar EFCC mai yaƙi da yi wa arziƙin ƙasa ta’annati ta gayyace shi kan zargin sha’anin kuɗi bayan wa’adinsa ya ƙare a matsayin mataimakin gwamnan Jihar Bayelsa.
A baya-bayan nan mawaƙin ya ce tsohon shugaban Najeriya ya taɓa zuwa EFCC a matsayin wanda aka yi wa tambayoyi ko gudanar da bincike a kan shi, sai dai wata sanarwa da tsohon shugaban ya fitar ta musanta hakan.
A jiya Juma’a ne Wealth Dickson Ominabo jami’in yaɗa labarai ne a ofishin tsohon shugaban ƙasar ya fitar da sanarwar da ta ƙaryata wannan iƙirari.
Inda ya ce ya yi amfani da wasu bayanai da wasu suka riƙa yaɗa wa a baya kan tsohon shugaban kasar domin su ɓata masa sunan, har suka riƙa cewa sai da ya je EFCC domin amsa tambayoyi.