Dangane da samar da aikin yi kuma Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya yi alƙawarin samar da aikin yi miliyan ɗaya a ɓangaren fasahar zamani.
Fasahar zamani aba ce wadda matasa suka fi cin gajiyarta, hakan ne ya sa Shugaban Nijeriyar ya ba da ƙarfi a ɓangaren fasahar zamanin,.
A cewar Shugaba Tinubu “Gwamnatina za ta ƙirƙiri damammaki ga matasa.
Za mu martaba ƙudurin da muka ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe na cewa za mu samar da guraben ayyuka miliyan ɗaya a ɓangaren fasahar zamani.”
“Za mu haɗa hannu da Majalisar Dokokin Tarayya wajen samar da dokar samar da ayyuka.
Dokar za ta sakar wa gwamnati mara wajen inganta hanyoyin samar da aikin yi…