Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ya haƙura da takarar neman shugabancin ƙasar a wa’adin mulki na biyu.
Shugaba Biden ya bayyana hakan ne a wani takataccen jawabi da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce ya bar takarar ne domin ”masalahar jam’iyyarsa da kuma ƙasarsa”.
Ya bayyana shekaru uku da rabi da ya yi yana jagorantar Amurka, ƙasar ta samu gagarumin ci gaba.
”A yau Amurka na da ƙarfin tattalin arziki a duniya, mun kafa tarihi a fannin zuba jari domin sake gina ƙasarmu” in ji shi.
Shugaba Biden dai na fuskantar mummunar hamayya daga tsohon shugaban kasar da ya kayar Donald Trump.
A baya-baya nan dai ana ta kiraye-kirayen Biden din ya hakura sakamakon shekaru da yanayi na rashin lafiya da ake zargin sun bayyana a jikinsa.