Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Adamawa, Bathiya, Ya Nada Mace a Matsayin Shugaban Masu Rinjaye

Kakakin majalisar dokokin Jihar Adamawa, Honarabul Bathiya Wesley, ya nada Kate Raymond Mamuno, a matsayin shugabar masu rinjaye na majalisar.

Wesley, ya sanar da haka ne a zaman majalisar na ranar Litinin, ya kuma bayyana dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Maiha Jingi Belel, a matsayin mataimakin shugaban masu rinjayen. Haka kuma kakakin majalisar ya bayyana mamba mai wakiltar karamar hukumar Yola ta Arewa, Suleiman Umar Alkali, a matsayin shugaban marasa rinjayen majalisar ta takwas.

Post masu alaƙa

Za a miƙa ƴan Najeriya da ake zargi damfara zuwa Amurka

Kotun majistare ta fara sauraren shari’ar sojan gona mai mukamin CSP 

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wanda ake zargi da damfarar mutane da cewa shi babban jami’in Dan sandan ne.