Home » Shugaban majalisar dokokin jihar Kano ya kaddamar da wasu kwamitoci 38

Shugaban majalisar dokokin jihar Kano ya kaddamar da wasu kwamitoci 38

by Anas Dansalma
0 comment
Shugaban majalisar dokokin jihar Kano ya kaddamar da wasu kwamitoci 38

A ranar Talata ne shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Alhaji Ismail Falgore, ya kaddamar da kwamitoci 38 domin gudanar da ayyukan sanya idanu ga aiyukan ɓangaren zartarwa a jihar.

Majalisar ta 10 ta kasance tana aiki da kwamitocin wucin gadi tun bayan kaddamar da ta a ranar 13 ga watan Yuni.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da taron, Falgore ya ce kwamitocin za su sanya ido kan ayyukan gwamnati a matsayin cikamakon aiyukan majalisar.

Falgore ya ce kwamitin da ke kula da asusun gwamnati zai kasance karkashin Alhaji Tukur Fagge; ayyuka da Gidaje, Muhammad Aliyu; Aminu Ungogo, Kudi; Ahmed Ibrahim; Noma.

Sauran sun hada da, Haruna Tahir, Albarkatun Ruwa; Alhassan Ishak, Lafiya; Suleiman Ishak, Ilimi; Shuaibu Rabiu, yada labarai da Ibrahim Muhammad, Karkara; da sauransu.

Kakakin majalisar ya shawarci shugabannin kwamitocin da Maida hankali wajen sauke nauyin da aka dora musu.

A Wani labarin kuma majalisar ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta kafa kwalejin ilimi a karamar hukumar Karaye.

Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa na jama’a da Ahmed Ibrahim (NNPP- Karaye) ya gabatar.

Da yake gabatar da kudirin, Ibrahim ya ce kwalejin, idan aka kafa ta za ta bunkasa harkar ilimi ga al’ummar yankin da jihar da ma kasa baki daya.

Dan majalisar ya kuma bayyana cewa hakan zai kara habaka tattalin arzikin yankin tare da samar da ayyukan yi ga matasan yankin.

A tasa gudunmawar mataimakin kakakin majalisar, Alhaji Muhammad Butu-Butu, (NNPP- Rimingado/Tofa) ya ce kwalejin idan aka kafa ta za ta magance matsalar karancin malamai a yankin.

Ya kuma ce makarantar za ta samar da ayyukan yi ga al’ummar Kiru da Bebeji da Karaye da Rimingado da kuma Tofa.

Bayan zaman da ‘yan majalisar suka yi, majalisar ta amince da kudurin, kuma ta bukaci gwamnatin jihar da ta kafa kwalejin ilimi a yankin.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi