• Home  
  • Shugaban Saliyo ya nemi afuwar waɗanda yaƙin basasa ya shafa bayan shekaru 24
- Babban Labari - Labarai

Shugaban Saliyo ya nemi afuwar waɗanda yaƙin basasa ya shafa bayan shekaru 24

Shugaban ƙasar Saliyo, Julius Maada Bio ya nemi afuwar waɗanda yaƙin basasa ya shafa bayan shekaru 24 inda ya amince da irin azaba da wahalhalun da al’umma suka fuskanta a lokacin da rikici ya addabi ƙasar daga shekarar 1991 zuwa 2002. Yaƙin ya yi sanadiyar mutuwar ɗaruruwan dubban mutane tare da barin dayawa da raunuka […]

Shugaban ƙasar Saliyo, Julius Maada Bio ya nemi afuwar waɗanda yaƙin basasa ya shafa bayan shekaru 24 inda ya amince da irin azaba da wahalhalun da al’umma suka fuskanta a lokacin da rikici ya addabi ƙasar daga shekarar 1991 zuwa 2002.

Yaƙin ya yi sanadiyar mutuwar ɗaruruwan dubban mutane tare da barin dayawa da raunuka masu tsanani.

Da yake jawabi a ranar Lahadi, shugaba Bio ya ce yana neman afuwa “a madadin ƙasa baki ɗaya,” yana mai amincewa da raɗaɗin da waɗanda suka tsira da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu suka fuskanta.

Ya ce lokaci ya yi da ƙasar za ta fuskanci abin da ya faru domin samun warkarwa da haɗin kai.

Jawabin ya zo ne a yayin bikin Ranar Tunawa ta Ƙasa ta farko ga waɗanda suka mutu a yaƙin basasar, inda wasu tsoffin sojoji, waɗanda aka yanke musu gaɓoɓi da sauran waɗanda rikicin ya shafa suka taru a tsohon ginin kotun musamman ta zaman lafiya a babban birnin ƙasar domin girmama waɗanda suka rasu.

Ana ɗaukar yaƙin basasar Saliyo, wanda ya yi sanadiyar mutuwar kusan mutum 120,000 tare da raunata da nakasa dubban mutane, ana ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin mafi munin rikice-rikicen zamani.

Rikicin ya ɗauki tsawon shekaru goma, kuma ya ƙare a hukumance a ranar 18 ga Janairu, 2002.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai