• Home  
  • NBRP ta yi alkawarin hada kai da hukumar NOA don kara sanya son karatu ga yan Nijeriya
- Babban Labari - Labarai

NBRP ta yi alkawarin hada kai da hukumar NOA don kara sanya son karatu ga yan Nijeriya

Hukumar wayar da kan al’umma ta ƙasa NOA tare da hadin gwiwa da Gamayyar Ƙungiyoyin Haɗin Kan Makaranta Littattafai da Raya Al’adar Karatu wanda a turanci ake kira Network of book club and reading culture suka yi tsari domin gina son kararu tare da samun Ingantaccen ilimi ga ‘yan kasa. ‎ ‎Da yake jawabi Amadadin […]

Hukumar wayar da kan al’umma ta ƙasa NOA tare da hadin gwiwa da Gamayyar Ƙungiyoyin Haɗin Kan Makaranta Littattafai da Raya Al’adar Karatu wanda a turanci ake kira Network of book club and reading culture suka yi tsari domin gina son kararu tare da samun Ingantaccen ilimi ga ‘yan kasa.
‎Da yake jawabi Amadadin shugaban hukumar Mallam Lanre Issa-Onilu, Daraktan sadarwa da yada labarai na hukumar Bala Musa, ya bayyana cewa hukumar tana kokari wajen inganta ilimi da dabi’u ma su kyau musamman ga matasan Najeriya.
‎Sannan ya kara da cewa matasa suna da rawar da za su taka wajen ci gaban kasa gamida raya al’adu.
‎A karshe ya bayyana kudirin gwamnatin tarayya na saka ilimin kishin kasa cikin manhajar karatu.
‎A nata jawabin sakatariyar NBRP Misis Ayotola Ilori ta bayyana gamsuwarsu da irin ayyukan da hukumar ke aiwatarwa a fadin kasar, sannan za su yi amfani da damar wajen bunkasa dabi’ar karatu a fadin Najeriya.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai