• Home  
  • Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi
- Babban Labari - Labarai

Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi

Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi, ya nemi ƙarin bayani kan dalilin ɗauke sojojin da ke gadin makarantar GGCSS Maga, gabanin harin da ’yan bindiga suka kai tare da sace ɗalibai 25. Gwamnan, ya ce gwamnati ta riga ta sanar da hukumomin tsaro game da yiwuwar kai hari, amma sojojin suka bar makarantar da misalin ƙarfe […]

Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi, ya nemi ƙarin bayani kan dalilin ɗauke sojojin da ke gadin makarantar GGCSS Maga, gabanin harin da ’yan bindiga suka kai tare da sace ɗalibai 25.

Gwamnan, ya ce gwamnati ta riga ta sanar da hukumomin tsaro game da yiwuwar kai hari, amma sojojin suka bar makarantar da misalin ƙarfe 3 na dare.

“An tura sojoji, amma sun bar makarantar da misalin ƙarfe 3 na dare, sannan ƙarfe 3:45 harin ya faru. Wa ya bayar da izinin su bar makarantar a wannan lokaci mai muhimmanci?” in ji Idris.

Ya ce bayan barin makarantar da sojoji suka yi ƙasa da awa guda ’yan bindiga suka kai hari.

Ya ce barin makarantar da sojojin suka yi, ya saɓa wa alƙawuran da aka yi na ƙarfafa tsaro a makarantu da ke kan iyakar jihar.

Idris, ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya da ta jihar na aiki tuƙuru don ceto ɗaliban da aka sace.

Gwamnan, ya bayyana cewa an umarci malaman addini da su yi addu’a domin samun zaman lafiya da kuɓutar da waɗanda aka sace.

Idris, ya ce abin da ya faru na nuna cewa akwai maƙiya da ke ƙoƙarin kawo cikas ga ci gaban jihar.

A yayin ziyarar nuna goyon baya, Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce abin da ya faru abin damuwa ne, musamman ma a lokacin da Kebbi ke samun ci gaba mai kyau.

Ya ƙara da cewa duk wani yunƙuri na daƙile ci gaban jihar ba zai yi nasara ba, kuma ya shawarci gwamnan da ya dage.

Ajaero ya ce, “Wannan kawo cikas ne, amma duk wani yunƙuri na daƙile ci gaban jihar ba zai yi nasara ba. Muna tare da ku.”

A halin yanzu, rundunar sojin ƙasa ta fara bincike kan dalilin da ya sa sojojin da aka tura makarantar suka bar wajen aiki kafin aukuwar harin.

Majiyoyin tsaro sun ce a yanzu haka an fara binciken wasu manyan jami’ai kan lamarin

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai