Sojoji Sun Halaka Yan Boko Haram Shida A Borno

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kisan mayaƙan Boko Haram shida a lokacin da suka daƙile wani hari da mayakan ƙungiyar suka yi yunƙurin kai wa wani sansanin soji a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Cikin wata sanarwa da Laftanar Kalan Sani Uba, jami’in hulda da jama’a na rundunar haɗin kai mai yaƙi da Boko Haram ya fitar, ya ce mayaƙan ƙungiyar sun shirya kai hari da asubahin yau kan sansanin sojin da ke Kangar a yankin Mallam Fatori.

”Da misalin ƙarfe 4:30 na asubahin yau Talata, 4 ga watan Nuwamba ne mayaƙan Boko Haram da na ISWAP, suka kitsa wani hari ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa da bindigogi kan sansanin soji, sai kuma nan take dakarunmu suka gaggauta mayar da martani tare da daƙile harin”, in ji sanarwar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, duk da jiragen marasa matuƙa da maharan suka yi amfani da su, dakarun Najeriyar ta hanyar taimakon sojojin sama sun samau nasarar fatattakar mayaƙan.

Bayan kammala fafatawar, bayanan da sojojin suka tattara sun tabbatar musu da mutuwar mayaƙan ƙungiyar shida da ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 biyar da manyan boma-bomai biyar da jirage marasa matuƙa huɗu masu ɗauke da boma-bomai, da gurneti 36 da nau’ikan alburusai masu yawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *