Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe kwamandojin ƙungiyar Boko Haram biyu tare da mayaƙa 11 yayin wani artabu na tsawon awanni a jihar Borno.
Kafar talabijin ta Channels TV ta ruwaito kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Manjo Janar Abdulsallam Abubakar yana bayyana Abu Nazir da Abu Fatima a matsayin jagororin da suka yi nasarar kashewa.
Ya ce mayaƙan ne suka yi yunƙurin kai hari a yankuna biyu na Bitta da Wulgo da ke ƙaramar hukumar Gwoza ranar Juma’a, inda suka daƙile su kuma suka kashe 13 daga cikinsu.
Ya ƙara da cewa fafatawar da suka yi ta ɗauki tsawon awanni, tun daga ranar Alhamis da dare har zuwa safiyar Juma’a.
A cewarsa, daga cikin kayayyakin da suka ƙwace a hannun ‘yanbindigar akwai babura shida, da bindigogi ƙirar AK-47 da yawa, da kuma ƙunshin harsasai.