Home » Tsohon Shugaban ‘Immigration’ Ya Ba Tinubu Shawara Kan Sha’anin Tsaro 

Tsohon Shugaban ‘Immigration’ Ya Ba Tinubu Shawara Kan Sha’anin Tsaro 

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment
NGO: An kaddamar da kundi kan yaƙi safarar bil’adama a Najeriya

Tsohon shugaban Hukumar Shigi Da Fici ta Najeriya ‘Immigration’ Muhammad Babandede ya shawarci shugaba Tinubu ya dawo da ƙwararrun sojojin ƙasar da suka yi ritaya bakin daga, domin yaƙar ‘yan ta’adda masu satar mutane da kuma ‘yan Boko Haram. 

Muhammad Babandede ya bayyana hakan ne yayin wani taron gidauniyar bunƙasa zaman lafiya karo na 21 da ya gudana a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.

Yayin jawabin sa, ya ce lokaci ya yi da gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta dawo da ƙwararrun zaratan sojojin ƙasar da aka yi wa ritayar gaggawa da sauran ƙuruciyarsu bakin daga domin cigaba da amfanar ƙasar ta fuskar tsaro; waɗan da yanzu da damansu suke zaune ba abin yi.

Babandede ya bada shawarar a ƙirƙiri runduna ta musamman a fannin tsaro domin a amfana da ƙwarewar sojojin da aka yi wa ritayar gaggawa.

Tsohon shugaban Hukumar Immigration ɗin ya ce,

“ Gwamnati ta kashe kuɗaɗe masu kauri wurin horas da zaratan sojojin ƙasar nan, amma da dama daga cikin su sun bar aiki a shekara 50 ko 55, sun koma gefe basa komai, waɗannan ƙwararru Kadarace a wurin Najeriya, ya zama wajibi a yi amfani da su”.

Haka zalika Babandede ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda zaratan sojoji ke barin aiki dan dole saboda an naɗa na ƙasa da su manyan muƙamai.

Ya ce “Suna tafiya kuma babu mai ƙara waiwayarsu”.

Dangane da haɗin kan ƙasa, Muhammad Babandede ya yi kira ga ‘yan siyasa da su guji amfani da ƙabilanci da addini wurin raba kan Najeriya.

Ya bayyana cewa akwai lokacin da ake zaune a Najeriya tsuntsaya maɗaurinki ɗaya, duk da cewa ba ƙabila ɗaya ce a ƙasar ba, ba kuma addini iri guda ake yi ba.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?