Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 6 a Adamawa

Dakarun rundunar Operation Haɗin Kai sun kashe wasu da ake zargin ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP shida yayin da daƙile harin da mayaƙan suka kai sansanin sojoji da ke Garaha, a Ƙaramar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa.

Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:07 na daren Litinin, 12 ga Oktoba, 2026, lokacin da maharan suka yi ƙoƙarin mamaye sansanin sojojin ta hanyar Lar.

Wata sanarwar da muƙaddashin mai magana da yawun rundunar, Kyaftin Mohammed Goni ya fitar ta ce dakarun Sashe na 4 sun fatattaki maharan ta hanyar amfani da dabarun yaƙi a yayin musayar wuta.

Rundunar ta ce binciken da aka gudanar bayan harin ya kai ga gano gawarwakin mayaƙa shida, da kuma makamai da alburusai.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Hong, Dakta Aliyu Yerima Sa’ad Hong, ya tabbatar da harin, inda ya ce jami’an tsaro, tare da taimakon masu gadin dazuka da mafarautan yankin, sun hana maharan cimma manufarsu.

Ya ce maharan sun kuma yi ƙoƙarin lalata wani turken sadarwa da ke ɗauke da kyamarorin sa ido da sojoji ke amfani da su wajen bibiyar ayyukan tsaro da gudanar da sintiri a yankin.

Sanarwar sojin ta ce kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindigogin AK-47 guda shida, ƙwanson harsashi 11, ɗaruruwan alburusai  ciki har da na musamman, bindigar PKT guda ɗaya da kuma bama-bamai masu girma.

Sauran kayayyakin sun haɗa da wayar hannu samfurin Android ƙirar Infinix, na’urar ɗaukar bidiyo ta Canon, jakunkunan ruwa guda uku, jakar ɗaukar bindiga da wasu tufafi.

Sai dai Sa’ad Hong ya ce an gano gawarwakin mayaƙa huɗu, duk da cewa wasu daga cikin maharan sun kwashe gawarwakin waɗanda aka kashe.

Ya ce ba a samu asarar ran fararen hula a Garaha ba, amma an ƙona shaguna biyu, yayin da sojoji biyu suka samu raunukan harbin bindiga.

Shugaban ƙaramar hukumar ya ƙara da cewa maharan sun kashe wani farar hula sannan sun ƙona wasu gidaje a ƙauyen Lar yayin da suke ƙoƙarin tserewa daga Garaha.

Rundunar ta ce sojojin da suka jikkata suna samun kulawar likitoci, yayin da ake shirye-shiryen kwashe su zuwa babban asibiti domin karɓar ƙarin magani.

Ta kuma ce dakarunta na ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro a yankin domin daƙile aukuwa wasu hare-haren.

Garaha, wadda mahaifar tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ce, na daga cikin yanki masu tsaunuka a Ƙaramar Hukumar Hong, kuma kusancinta da dajin Sambisa na daga cikin abubuwan da ke ƙara tayar da hankalin tsaro a yankin.

Post masu alaƙa

NDLEA Ta Kama Mutane 1,860, Ta Kwace Ton 5.4 na Miyagun Ƙwayoyi a Kano.

Jami’ar Azare Za Ta Bai Wa Tsohon Ministan Ilimi, Adamu Adamu, Digirin Girmamawa

Yan sanda sun kama mutane 4 tare da ƙwato motocin sata a Kano