Sojojin Najeriya sun ce sun tseratar da matafiya 23 daga masu garkuwa a Kogi

Rundunar sojin ƙasan Najeriya ta ce jami’anta sun samu nasarar tseratar mutum 23, waɗanda ta ce matafiya ne da ƴanbindiga suka tare a babbar hanyar Ayegunle zuwa Bunu da ke jihar Kogi, kamar yadda jaridar Guardian mai zaman kanta ta ruwaito a ranar Asabar 6 ga Yuni.

Rahotanni sun bayyana cewa ƴanbindiga sun tare hanyar ne domin sace mutane, amma sojoji suka kai agajin gaggawa bayan sun samu kiran kar-ta-kwana, inda suka isa wajen cikin lokaci suka fatattaki ƴanbindigar tare da tseratar da matafiyan.

Rahoton ya ƙara da cewa maharan sun tsere da suka ga isowar sojoji, “amma duk da haka sojojin sun bi bayansu domin farautarsu a cikin dajin.”

Sai dai jaridar ta ruwaito cewa mutum biyu sun rasu harin, sannan wasu biyar sun samu rauni.

Post masu alaƙa

Yar Najeriya ta kammala jami’ar Burtaniya da daraja ta daya (1st Class) a ilimin kimiyar samar da manhajar kasuwancin zamani.

A riƙa yi wa masu shirin aure gwajin miyagun ƙwayoyi :- Buba Marwa

Bwala yayi zargin akwai hannun kasashen wajen kan matsalar tsaro a Nijeriya