‘Yan Arewa mazauna jihohin Kudu maso Yammacin Najeriya sun koka kan abin da suka bayyana a matsayin yawaitar tsangwama da nuna musu wariya sakamakon matsalolin tsaro da yankin ke fuskanta.
Shugaban Ƙungiyar Taimakon Ci gaban Arewa a Jihar Osun, Ahmad Salihu, ya ce fargabar hare-haren masu garkuwa da mutane ta sa ana zargin ƴan Arewa da aikata laifuka ba tare da hujja ba.
Ahmad Salihu ya ce a kwanakin baya wasu matasa shida daga Arewa sun tsallake rijiya da baya bayan da aka yi yunƙurin kashe su a garin Ile-Ife, saboda an yi zargin cewa ƴan bindiga ne.
A cewarsa, matasan sun biyo motar dakon dabbobi zuwa Jihar Osun, sai suka yi ƙura da datti, abin da ya jawo wasu suka yi musu mummunar fahimta.
Salihu ya yabawa jami’an ƴan sa-kai saboda saurin shiga tsakani da suka yi, inda suka ceci matasan tare da miƙa su ga shugabannin al’ummar Hausawa bayan an tabbatar da cewa matafiya ne ba ‘yan ta’adda ba.
Shugaban Ƙungiyar Taimakon Ci gaban Arewa a Jihar Osun, Ahmad Salihu ya yi kira ga ƴan Arewa masu tafiya yankin Kudu maso Yamma da su yi taka-tsantsan tare da kauce wa abubuwan da za su iya jawo zargi a kansu.
Haka kuma, wani jagoran Fulani a Jihar Ekiti, Malam Zayyanu Muhammad, ya ce ana yawaita kama da tsangwamar Fulani da Hausawa, musamman matafiya da masu kiwon dabbobi, sakamakon matsalolin tsaro da ake fama da su.
A wani lamari makamancin haka a Jihar Legas, rundunar ƴan sanda ta ƙaryata rahotannin da suka yaɗu a kafafen sada zumunta cewa ƴan bindiga sun kai hare-hare a wasu yankuna na jihar. Rundunar ta ce wannan jita-jita ce da ta haifar da mutuwar wani matashin mai babur mai suna Kulaha Ayuba, inda aka yi masa kisan gilla bisa zargin cewa ɗan bindiga ne.
Ƴan sanda sun ce sun kama mutum 15 da ake zargi da hannu a lamarin, tare da gargaɗin cewa za a hukunta duk wanda ya ƙirƙira ko ya yaɗa labaran ƙarya da ka iya haddasa tashin hankali ko rikicin ƙabilanci.