Sojojin Najeriya sun ceto mutane 9 daga masu garkuwa a Kogi.

Sojojin Najeriya sun ceto mutane tara, ciki har da jariri, bayan arangama da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a kan hanyar Ajaokuta zuwa Itobe a Jihar Kogi.

Dakarun Bataliya ta 21 sun bi sawun masu garkuwar har zuwa kusa da Adumu, inda suka yi musu luguden wuta, lamarin da ya tilasta musu tserewa tare da barin wadanda suka yi garkuwa da su.

Daga cikin wadanda aka ceto akwai tsofaffi maza biyu, tsofaffi mata biyu, maza hudu da jariri.

An mika wadanda aka ceto ga yan sanda a Itobe, yayin da sojojin ke ci gaba da neman sauran wadanda ake zargin an yi garkuwa da su.

 

Post masu alaƙa

Atiku ya naɗa El-Rufai cikin mambobin kwamitin yaƙin zaɓensa

Yara mata 4 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa

Ba na jin haushin abokaina da suka yi shiru kan tsare ni — El-Rufai