Kotu tsare mutane biyu da ake zargi da rushe Gadar Watari da yanka filaye ba bisa ka’ida ba a Kano.

Kotun Majistare mai lamba 47 da ke Unguwar Zangero a Jihar Kano, ta bayar da umarnin tsare wasu mutane biyu a gidan gyaran hali bisa zarginsu da hannu a rushe Tsohuwar Gadar Watari tare da kwashe kayan ginin gadar da kuma yanka filaye ba bisa ka’ida ba.

Jami’an tsaron farin kaya na DSS ne suka gurfanar da mutanen biyu, Danlami Sulaiman, wanda aka fi sani da Layayu, da Abdullahi Ibrahim, wanda aka fi sani da Maraki, a gaban kotun. Ana zargin mutanen biyu da laifukan hada baki, sata, ƙeta da kuma shiga wani wuri ba tare da izini ba.

A ranar 22 ga watan Yuli, 2026, wadanda ake zargin sun je wata gada da ke yankin Danjirima, a Karamar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano, inda ake zargin sun rushe gadar tare da kwashe rodi da karafan da ke jikinta.

Haka kuma, ana zargin sun yi amfani da wurin wajen yanka filaye ba tare da izinin hukumomin da abin ya shafa ba.

Bayan da magatakardar kotun ya karanta musu tuhume-tuhumen da ake yi musu, wadanda ake zargin sun musanta aikata laifukan. Alkalin kotun, Mai Shari’a Abba Maiwada Abubakar, ya bayar da umarnin a tsare su gidan gyaran hali, inda za su ci gaba zuwa ranar 8 ga watan Satumba, 2026, domin ci gaba da sauraron shari’ar

Post masu alaƙa

Sojojin Najeriya sun ceto mutane 9 daga masu garkuwa a Kogi.

Rundunar yan sandan Kano ta kwato motar da aka sace sannan aka siyar da ita a Nijar

Gwamnatin Tarayya za ta biya tsofaffin ma’aikatan da ta sallama shekaru 20 da suka gabata