Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya amince da kafa kwamitin yakin neman zabensa na shugaban kasa, wanda zai kasance ƙarƙashin jagorancin Kashim Ibrahim-Imam sai Nasir El-Rufai a matsayin mataimakinsa.
Naɗin na zuwa ne yayin da El-Rufai ke tsare a hannun hukumomi bisa tuhume-tuhumen da gwamnati ke yi masa.
Daraktan yaɗa labarai na kwamitin, Phrank Shaibu, wanda kuma shi ne babban mataimaki na musamman ga Atiku kan harkokin sadarwa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
Sanarwar ta ce an tsara kwamitin ne bisa la’akari da halin tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fuskanta, ciki har da tashin farashin kayan masarufi da tsadar sufuri da kuma raguwar kudaden shiga.
An nada Sanata Austin Akobundu a matsayin babban daraktan yakin neman zaben, wanda zai jagoranci aiwatar da dabarun kwamitin cikin tsari.
Haka kuma, mataimakan babban darakta shida za su kula da harkokin gudanarwar kwamitin, inda za su yi aiki tare da daraktoci 30 da aka ɗorawa nauyin kula da fannoni daban-daban.
Dele Momodu ne zai shugabanci harkokin yaɗa labarai da sadarwa yayin da Dino Melaye kuma zai jagoranci sashen tuntuɓa.
Shi kuma Mohammed Hayatudeen zai jagoranci kwamitin tsara manufofi tare da Farfesa Mohammed Sagagi da wasu mambobi kamar Farfesa Kingsley Moghalu.