• Home  
  • Sojojin Najeriya Sun Halaka Yan Fashin Daji A Zamfara
- Babban Labari - Labarai

Sojojin Najeriya Sun Halaka Yan Fashin Daji A Zamfara

Rundunar sojan sama ta Najeriya ta ce ta yi nasarar kashe ‘yanfashi da dama waɗanda ba ta faɗi adadinsu ba a garin Tsafe na jihar Zamfara bayan wani hari ta sama. Mai magana da yawun rundunar,,Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce an kai hare-haren ne kan sansanin ‘yanfashi na Sauri ranar Juma’a bayan tattara bayanan […]

Rundunar sojan sama ta Najeriya ta ce ta yi nasarar kashe ‘yanfashi da dama waɗanda ba ta faɗi adadinsu ba a garin Tsafe na jihar Zamfara bayan wani hari ta sama.

Mai magana da yawun rundunar,,Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce an kai hare-haren ne kan sansanin ‘yanfashi na Sauri ranar Juma’a bayan tattara bayanan siri.

Ya ce bayanai sun tabbatar da ‘yanbindigar na karakaina a wurin da suka ɓoye shanun sata da ke kan wani tsauni da ke ba su kariya da kuma ajiye kayayyaki.

“An kai hare-hare da dama waɗanda suka dira kan ‘yanfashin da ke yunƙurin guduwa cikin duhun daji, inda aka bi su kuma aka kashe su,” in ji sanarwar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000