• Home  
  • Babu Janar Din Da ISWAP Ta Kama A Borno — Sojoji
- Babban Labari - Labarai

Babu Janar Din Da ISWAP Ta Kama A Borno — Sojoji

Rundunar Soji ta ƙaryata rahotannin da ke cewa an yi garkuwa da kwamandan Bitget ta 25 da ke Jihar Borno a wani harin kwanton ɓaunan mayaƙan ƙungiyar ISWAP. Ta buƙaci jama’a su yi watsi da wannan labarin ƙarya, tare da yin addu’ar samun nasarar sojojin Najeriya da ke bakin daga. Rundunar ta ce sojojin sun […]

Rundunar Soji ta ƙaryata rahotannin da ke cewa an yi garkuwa da kwamandan Bitget ta 25 da ke Jihar Borno a wani harin kwanton ɓaunan mayaƙan ƙungiyar ISWAP.

Ta buƙaci jama’a su yi watsi da wannan labarin ƙarya, tare da yin addu’ar samun nasarar sojojin Najeriya da ke bakin daga.

Rundunar ta ce sojojin sun murƙushe wani harin kwanton ɓauna da ISWAP ta kai musu a yayin da suke sintiri domin kare al’ummomin da ke kewaye da Wajiroko a yankin Azir Multe a Ƙaramar Hukumar Damboa da ke Jihar Borno.

Ta ce sojojin sun gamu da kwanton ɓauna ne daga ’yan ta’adda yayin da suke dawowa daga aikin sintiri a gefen Dajin Sambisa.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000