Sojojin sun kashe ‘ƴan ta’adda’ tare da ƙwace abubuwan fashewa 180 a Zamfara

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation FANSAN YAMMA sun kashe wasu ‘yan ta’adda tare da kwace makamai da kuma kama wani da ake zargin yana kai wa ‘yan ta’adda kayan fashewa guda 180 a jihar Zamfara.

A cewar wata sanarwa da rundunar ta fitar, dakarun sun yi arangama da ‘yan ta’addan ne a yankin Garin Kaso da ke ƙaramar hukumar Birnin Magaji yayin wani samame da suka kai.

An kashe biyu daga cikin ‘yan ta’addan tare da kwace bindigogi biyu, alburusai da babura biyu.

Sanarwar ta ƙara da cewa yayin da samamen ke ci gaba, wasu ‘yan ta’addan sun yi ƙoƙarin yi wa sojojin kwanton bauna daga maɓoyarsu, amma dakarun sun samu nasarar daƙile harin tare da tilasta musu tserewa.

Rahotanni daga al’ummomin yankin sun nuna cewa an kwashe gawarwaki da kuma waɗanda suka jikkata daga cikin ‘yan ta’addan bayan artabun.

Post masu alaƙa

INEC ta kai wa CBN ajiyar muhimman kayan zaɓen Gwamnan Osun

Hisbah za ta fara farautar masu aikata baɗala a Kano

Kwastam ta kama harsasai 3,300 da kayayyakin fasa-ƙwauri a Seme