Tinubu na kan hanyar komawa Najeriya bayan kammala hutun aiki

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kammala hutun aiki da ya ɗauka kuma tuni ya kamo hanyar komawa gida daga birnin Paris na Faransa.

Cikin wata sanarwa da fadar shugaban Najeriyar ta fitar, ana sa ran jirgin shugaban ƙasar zai sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas da yammacin yau.

Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya zaɓi ya sauka a Legas domin girmama marigayi Cif MKO Abiola, wanda ake kallonsa a matsayin gwarzo a gwagwarmayar dimokuraɗiyyar Najeriya.

A ranar bikin samun ’yancin kai, shugaba Tinubu zai halarci bikin haska wani fim da aka shirya domin karrama Abiola, wanda ya lashe zaɓen watan Yunin 1993 wanda za a nuna a Legas.

Sanarwar ta bayyana cewa yayin zamansa a Legas, Shugaba Tinubu zai kuma gana da jagororin siyasa da abokan hulɗarsa na tsawon kwanaki, a wani ɓangare na shirye-shiryen zaɓen 2027.

A ranar 30 ga Agusta ne Shugaba Tinubu ya bar Abuja domin hutun aiki. Ya shafe mako guda a Landan kafin ya wuce Paris da ke Faransa.

Yayin zamansa a Paris, Tinubu ya halarci liyafar cin abinci da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa. Ya kuma gana da ’yan kasuwa, ciki har da Vincent Bolloré.

A ranar Litinin, Tinubu ya kuma gana da shugaban First Holdings, Femi Otedola.

A makon da ya gabata, Shugaba Tinubu ya shaida rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatin Jihar Ogun da DP World, domin gina tashar jiragen ruwa mai zurfi ta Gateway a Ogun.

Sanarwar ta kuma ce Tinubu zai koma Abuja da zarar ya kammala hidindimunsa na siyasa a Legas.

Post masu alaƙa

An yanke wa mutum hudu hukuncin kisa kan satar mutane a Najeriya

INEC ta sanar da ranar fara karɓar katin zaɓe na PVC a faɗin Najeriya

Dangote, Habasha da Djibouti za su gina bututun mai na dala miliyan 600