Gidauniyar da ke tallafawa marayu, zawarawa da masu ƙaramin ƙarfi ta SURE4U ta biyawa yara 27 Kuɗin makaranta sama da Nair Miliyan ɗaya da rabi na shekara guda a Cibiyar Nazarin Harshen Larabci Da Darussan Addinin Musulunci (CAIS) da ke a Abuja.
Babban daraktan makarantar, Alhaji Salihu Bala ne ya bayyana hakan yayin walimar da aka shirya wa ɗaliban makarantar a ranar Lahadi 20 Oktoba, 2024.
Yayin gabatar da daliban, Alhaji Salihu Bala ya bayyana cewa yaran da SURE4U ta ɗauki nauyin karatunsu sun cancanci a ɗauki nauyinsu, kuma ba dan Allah ya taimaka an ɗauki nauyinsu ba, to ba za su iya zuwa makaranta ba.
Alhaji Muhammad Babandede OFR, OCM shugaban gidauniyar SURE4U kuma jagoran kwamitin harkokin intanet da tsaro na Ƙungiyar Musulmi Ta Abuja da ke babban masallacin Fouad Lababidi (MCC) wurin da CAIS na daga cikin waɗan da suka halarci walimar.
Alhaji Babandede ya ce basu san kowa ba daga yaran da suka biya wa kuɗin makaranta ba, fatansu shine yaran su amfana da abin da su kayi.
Ya kuma buƙaci sauran jama’a da ƙungiyoyi masu zaman kansu su biyo bayansu wurin wannan babban aiki domin inganta rayuwar matasa.
Ya ƙara da cewa, “ Duk yadda za a yi ƙoƙari wurin yaƙar rashin tsaro idan ba a ɗauki matakin ilimantar da yaran da marayu masu ƙaramin ƙarfi ba, za a yi ta yi ne kamar ba a yi.
Shugaban tafiyar MCC Sanata UK Umar Sarkin Kibiya da ya samu wakilcin Alhaji Abubakar Dallatun Katsina ya jinjinawa mamallakin gidauniyar SURE4U Alhaji Muhammad Babandede.
Sanata ta ya yi addu’a da fatan alkhairi ga SURE4U, ya kuma yi fatan sauran masu ƙarfi da kungiyoyi masu zaman kansu suma za su bada gudunmawa wurin inganta rayuwar marasa ƙarfi.