ASUU ta nemi gwamnati ta biya malaman jami’o’i albashin da aka riƙesu
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU ta sake buƙatar gwamnatin tarayya ta biya albashin da aka riƙe wa malamai tare da warware sauran matsalolin jin daɗin ma’aikatan jami’o’i. Shugaban ASUU, Farfesa Christopher Piwuna, ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a Jami’ar Jos, inda ya ce gwamnati ta cika sauran sharuddan yarjejeniyar da ta ƙulla […]





