Borno

Sojoji sun ceto Kansila da malami da aka sace a Borno

Sojojin Najeriya a ƙarkashin Operation Hadin Kai sun ceto fararen hula biyu da ‘yan ta’adda suka sace a kan hanyar Buni Gari-Buratai da ke Borno, bayan wani aikin bincike da ceto cikin gaggawa da ake gudanarwa. Majiyoyi sun shaida cewa, sojojin rundunar 27 Task Force Brigade tare da haɗin gwiwar rundunar 135 Special Forces Battalion […]

Read more

Sojoji sun daƙile yunƙurin harin ƴanbidiga a Borno

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta na Operation Haɗin Kai daƙile yaƙunrin hain ƴanbindiga ina sun kashe su daga tsaunukan Mandara a lokacin da suka yunƙurin kai hari a cikin al’ummar Bitta da ke Borno. Rundunar ce ta sanar da hakan a shafinta na X inda ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe […]

Read more

Nakiya ta hallaka yara 4 a Borno

Wata nakiya da ta fashe a garin Banki, da ke Ƙaramar Hukumar Bama, a Jihar Borno, ta yi sanadin mutuwar yara huɗu tare da jikkata wani yaro guda ɗaya. Rundunar ’yan sandan jihar, ta tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Juma’a. Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 12:40 na rana a bayan tashar motar Banki […]

Read more

ISWAP ta kashe kwamandan sojan Najeriya a Borno

Mayaƙan ƙungiyar ISWAP da ke kai hare-hare a jihar Borno sun kashe wani kwamandan sojin saman Najeriya, bayan samun damar katse bayanan wurin da sojojin suke a tsakanin Damboa da Biyu da jihar. Jaridar PR Nigeria ta rawaito cewa sojan shi ne kwamandan da ke jagorantar rundunar da ta kai wa sojojin haɗin gwiwa na […]

Read more

Babu Janar Din Da ISWAP Ta Kama A Borno — Sojoji

Rundunar Soji ta ƙaryata rahotannin da ke cewa an yi garkuwa da kwamandan Bitget ta 25 da ke Jihar Borno a wani harin kwanton ɓaunan mayaƙan ƙungiyar ISWAP. Ta buƙaci jama’a su yi watsi da wannan labarin ƙarya, tare da yin addu’ar samun nasarar sojojin Najeriya da ke bakin daga. Rundunar ta ce sojojin sun […]

Read more

An ceto mutane 86 daga hannun ’yan ta’adda a Borno

Rundunar sojin Operation Hadin Kai (OPHK) da ke yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas ta sake samun nasara bayan ta ceto mutane 86 da kuma kama wasu mutum 29 da ake zargi da samar wa ’yan ta’adda kayayyaki a Jihar Borno. A cewar sanarwar da Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanar Kanar […]

Read more

Sojoji Sun Halaka Yan Boko Haram Shida A Borno

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kisan mayaƙan Boko Haram shida a lokacin da suka daƙile wani hari da mayakan ƙungiyar suka yi yunƙurin kai wa wani sansanin soji a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya. Cikin wata sanarwa da Laftanar Kalan Sani Uba, jami’in hulda da jama’a na rundunar haɗin kai mai […]

Read more