Sojoji sun ceto Kansila da malami da aka sace a Borno

Sojojin Najeriya a ƙarkashin Operation Hadin Kai sun ceto fararen hula biyu da ‘yan ta’adda suka sace a kan hanyar Buni Gari-Buratai da ke Borno, bayan wani aikin bincike da ceto cikin gaggawa da ake gudanarwa.

Majiyoyi sun shaida cewa, sojojin rundunar 27 Task Force Brigade tare da haɗin gwiwar rundunar 135 Special Forces Battalion da kuma ‘yan ƙungiyar Sibiliyan JTF ne suka ceto su.

Majiyoyin Rundunar Soja sun ce, an fara aikin ceton ne da misalin ƙarfe 7:35 na safe a ranar Laraba bayan sace fararen hula bakwai da misalin ƙarfe 5:00 na yamma a ranar Talata a kan titin Buni Gari-Buratai.

“Saboda haka, da misalin ƙarfe 11:35 na safe a ranar Laraba, sojoji sun gano mutane biyu da aka sace waɗanda ‘yan ta’addan suka yi watsi da su bayan sun ji motsin sojoji zuwa wurin da suke gaban ƙauyen Mangari,” in ji majiyar.

Kamar yadda majiyar ke cewa, waɗanda aka ceto sun haɗa da: Alhaji Mohammed Ali Maiakachi, wani

Kansila mai wakiltar Mazaɓar Zera/Wuyep Ward a ƙaramar hukumar Biu, da kuma Malam Aliyu Yusuf wani malamin addinin Musulunci kuma shugaban Shuaaraul Islam, Jihar Borno.

A cewar majiyar, sojojin sun tabbatar da sakin waɗanda abin ya shafa nan take sannan suka bi ‘yan ta’addan da suka gudu na tsawon kimanin kilomita 5.4, amma ba akai ga cimma su ba.

An ruwaito cewa, waɗanda aka ceto sun sanar da sojoji cewa har yanzu ana tsare da wasu fararen hula biyar, ciki har da tsofaffin mataimakan shugaban ƙaramar hukumar Biu na baya da na yanzu da kuma mata uku.

Majiya ta ƙara da cewa, “Ana ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran fararen hula biyar ɗin da ke hannun su.”

Kamar yadda rahoton ke nunawa da farko an kai waɗanda abin ya shafa zuwa wurin karɓar magani domin duba lafiyar su kafin a mayar da su Biu, inda za su sake haɗuwa da iyalansu.

 

Post masu alaƙa

Jigawa Za Ta Bai Wa Alhazai Abinci Sau Uku a Rana a Hajjin 2026

Namadi Ya Kaddamar da Shirin Fadada Ilimi yayin da SLU ta Yaye Dalibai Sama da 4,000

Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Jigawa Ta Taya Gwamna Namadi Da Musulmi Murnar Eid-el-Fitr