Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bayyana matuƙar alhini ga gwamnatin jihar Borno da mutanen Darajamal kan harin ‘yan bindigar da ya yi sanadiyyar rayukan mutane da dama a ƙaramar hukumar Bama.
Shettima ya ce wannan lamari babban rashi ne ga jihar da kuma ƙasa baki ɗaya.
A cikin sakon ta’aziyya da ya tura ranar Litinin, mataimakin shugaban ƙasan ya ce: “Ina mika ta’aziyyata ga gwamna Babagana Umara Zulum da jama’ar Borno, da sojojin Najeriya kan wannan rashi mai girma.
Mutuwar waɗannan ‘yan ƙasa ta girgiza dukkan Najeriya, amma muna da tabbacin cewa adalci zai tabbata ga iyalan mamatan.”
Shettima ya bayyana cikakken goyon bayansa ga karfin sojojin Najeriya wajen shawo kan ƙalubalen tsaro da jihar ke fuskanta, inda ya jaddada umarnin shugaba Bola Ahmed Tinubu na sayen ƙarin jirage yaƙi marasa matuƙa tare da umarnin inganta dabaru da canza salo wajen fatattakar waɗannan ƴan bindiga.
Mataimakin Shugaban Kasan ya kuma yi magana kan batun kafa ‘yan sanda na jihohi, inda ya bayyana cewa Tinubu yana ganin cewa wasu jihohin Najeriya na buƙatar kungiyoyi na musamman da za su fahimci yanayin ƙasa da al’adu, da kuma iya yin aiki tare da jama’a a matakin ƙauye.
Shettima ya kuma yi alƙawarin ci gaba da tallafawa gwamnatin jihar Borno da iyalan da abin ya shafa wajen shawo kan matsalolin tsaro, tare da tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da ba da goyon baya cikin duk matakan da za su kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga.