APC ta fara faɗawa tarkon rikici a jihar Kano
Kurar rikici ta fara turnuƙewa a jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kano, da ke arewacin Najeriya, makonni bayan sauyin sheƙar gwamna Abba Kabir Yusuf. An fara ganin ƙurar ne a tarukan haɗa kan ‘ya’yan jam’iyyar APC tsoffi da sabbi a cikin wasu ƙananan hukumomin jihar. Shugabancin APC ne ya ba da umarnin gudanar da […]









