Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Kaduna ta ɗage sauraron buƙatar belin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, zuwa ranar 31 ga Maris, 2026.
An ɗauki wannan matakin ne bayan zaman kotun na ranar Talata, inda ɓangaren masu ƙara da masu kare kai suka gabatar da hujjoji.
A zaman kotun, lauyan El-Rufai, Ukpon Akpan ya buƙaci kotun da ta ba da belin tsohon gwamnan, yana mai cewa hakan na cikin haƙƙinsa a kundin tsarin mulki, tare da buƙatar samun isasshen lokaci domin shirya kare shi a kotu.
Sai dai ɓangaren masu ƙara sun yi adawa da buƙatar, suna mai cewa tuhume-tuhumen da ake yi wa El-Rufai masu nauyi ne, kuma bayar da beli na iya kawo cikas ga binciken da ake ci gaba da yi.
Alƙalin kotun ya ɗage sauraron buƙatar neman beli zuwa ranar 31 ga watan Maris, bayan da mai gabatar da ƙara na ICPC ya ce idan aka bayar da belin tsohon gwamnan to zai iya lalata shari’ar.
Hukumar ICPC ce ta gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kotu bisa zargin cin hanci da kuma amfani da mukami ba daidai ba.