El-Rufai ya sake gurfana a kotun Kaduna

Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya sake gurfana a gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna a ranar Talata kan tuhumomin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ta shigar a kansa.

An gurfanar da El-rufai ne kan laifuka da suka hada da amfani da mukami ba bisa ka’ida ba, damfara, da bai wa wasu dama fiye da yadda ya dace, da kuma wasu tuhumomi da suka shafi kudade.

El-Rufai ya bayyana a kotun ne bayan ICPC ta sake shi daga tsare shin da tayi na fiye wata guda, wanda hakan ya biyo bayan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Ummar El-Rufai, a Cairo, Masar..

Bayan kammala gurfanan sa a Babbar Kotun Jihar, za a kai El-Rufai Kotun Tarayya da ke Kaduna, inda za a fara sauraron buƙatar belinsa da ya shigar.

Ana sa ran cewa za a duba batun belinsa cikin gaggawa, saboda irin nauyin tuhumomin da ake masa.

Post masu alaƙa

PDP ce za ta lashe zaɓen 2027 a Jigawa — Sule Lamido

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Ƙungiyar agoya bayan  shugaba Tinubu a zargi yan Daba da hana ta kai tallafi ga marasa galihu a Bauchi .