Kaduna

NiMet Ta Yi Hasashen Samun Hazo A Wasu Jihohin Najeriya

Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya, NiMet ta yi hasashen samun mabambantan yanayi a wasu sassan ƙasar, da suka haɗa da hazo da ruwan sama daga Litinin zuwa Laraba. Cikin wani rahoto da hukumar ta fitar ranar Lahadi ta buƙaci ƴanƙasar su zama cikin shiri domin tunkarar waɗannan yanayi. NiMet ta yi hasashen samun hazo […]

Read more

Masu Kwacen Waya Sun Kashe Ma’aikaciyar Lafiya A Zariya

Wasu da ake zargin masu kwacen waya ne sun kashe ma’aikaciyar jinya a Asibitin Gambo Sawaba da ke Zariya a jihar Kaduna mai suna Hadiza Musa. Bayanai sun ce marigayiyar it ace mataimakiyar shugabar sashen haihuwa a asibitin. Mijinta, Hamza Ibrahim Idris, wanda ke aiki a Abuja, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kashe matarsa […]

Read more

An Kama 26 Da Ake Zargin Masu Garkuwa Ga Mutane

Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta kama wasu mutane 26 da ake zargi da yin garkuwa da mutane, tare da ƙwato bindigogi guda 4, da muggan makamai da dama. Ta kuma kama wani ɓangare na kuɗin fansa da ake zargin an biya masu garkuwa da mutane a wasu hari daban-daban a jihar. Nasarar kamen dai […]

Read more

Mamakon Ruwan Sama Ya Hallaka Dalibai 2 Da Yarinya A Zariya

Wani mamakon ruwan sama da aka tafka a birnin Zariyan jihar Kaduna, ya yi sanadiyar mutuwar mutum uku yayin da kuma ake ci gaba da neman gawar mutum daya. Bayanai sun nuna cewa biyu daga cikin wadanda suka rasa ransu dalibai ne, Fatima Sani Danmarke mai shekara 18, da ke karatu a makarantar share fagen shiga jami’a da ke Funtua a jihar Katsina da Yusuf Surajo da shi […]

Read more

Uba Sani Yaro Na Ne A Siyasa Ba Aboki Ba – El-Rufi

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce Gwamnan Kaduna, Uba Sani bai abokinsa ba ne, kawai yaronsa ne na siyasa. El-Rufai ya bayyana haka ne a zantawarsa da tashar Channels, inda ya ƙara da cewa yanzu ba sa magana da gwamnan mai ci, “saboda duk wajen da na bari bayan na gama aikina, ba na […]

Read more

Kwastam Ta Kama Tabar Wiwi Ta Naira Miliyan 48.5 A Kaduna

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta bayyana cewa jami’anta sun kama tabar wiwi mai darajar naira miliyan 48.5 da wasu kayan da aka haramta na naira miliyan 220 a Jihar Kaduna kamar yadda Gidan talabijin na Channels ya ruwaito. Kwamandan hukumar ya ce an kama kayayyakin ne a ayyuka daban-daban da aka gudanar ranar 21 ga […]

Read more