Dan KAROTA da direba ya buge ya gudu Nasiru Abdullahi Mai Jihadi ya rasu ya bar mata 2 da ‘ya’ya 12.

Rahoto daga Dambatta ya tabbatar da cewa jami’in kula da cinkoson ababen hawa a jihar Kano KAROTA Nasiru Abdullahi Mai Jihadi da wani direba ya buge har ya samu karaya 6 ya rasu.
Yayan Nasiru Abdullahi Mai Jihadi, Abdulqadir Mai Dawa ya tabbatar da rasuwarsa ga Shamsi Umar Bakanike Dambatta, inda ya ce ya rasu ya bar yara 12 da mata biyu.
Kungiyar dirobobi da ‘yan uwan Dan KAROTA sun bayyana alhininsu dangane da rasuwar sa, kuma sun bayyana shi a matsayin mutum mai mu’amala da sanin ya kamata.
An yi jana’izar Mai Jihadi kamar yadda addinin musulunci ya tanadar

Post masu alaƙa

An kama budurwa ‘yar shekara 15 kan safarar miyagun kwayoyi a Delta.

Uwargidan shugaban Najeriya Sanata Oluremi Tinubu ta kaddamar da rumbum abinci ga jama’ar kudu maso kudancin Najeriya.

Kwamandan NSCDC ya gana da mahukuntan tashar tsandauri ta Dala Dry Port Kan inganta tsaro.