Yan sanda da INEC sun yaba da yadda zaɓen Dawakin Kudu ke gudana a Kano.

Rundunar yan sandan jihar Kano da INEC sun yaba da yadda zaɓen cike gurbin majalisar dokokin Jihar Kano mai wakiltar Dawakin Kudu ke gudana cikin lumana.

Kwamishinan ’yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, tare da kwamishinan hukumar zaɓe ta INEC a Kano, Ambasada Zango Abdu, sun duba rumfunan zaɓe domin tantance tsaro da yadda ake gudanar da zaɓen.

Kakakin ’yan sandan Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce kawo yanzu babu wata matsala da aka fuskanta, yayin da jami’an tsaro za su ci gaba da kasancewa a rumfunan zaɓe har zuwa kammala tattara da bayyana sakamako.

INEC ta kuma yaba wa jami’an tsaro da al’ummar Dawakin Kudu kan haɗin kai da bin doka da oda.

Post masu alaƙa

An dakatar da shugaban NSCDC a Neja kan mutuwar masu haƙar ma’adanai 37

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta raba wa iyalan jami’anta 62 sama da Naira miliyan 34

Gwamnan Kano ya naɗa Barista Hafsat Kutama shugabar hukumar PCACC