Kebbi

An kama mutum 4 kan damfarar maniyyata a Kebbi

Wasu mutum huɗu da ake zargi da damfarar maniyyata aikin Hajjin bana sun shiga hannu a Jihar Kebbi. Jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta, SP Bashir Usman, ya bayyana cewa dubun waɗanda ake zargin ta cika ne bayan ƙorafe-ƙorafe daga waɗanda abin ya shafa da kuma Hukumar Jin Daɗin Alhazai […]

Read more

Sanata ya bar APC a jajibirin zaɓen fidda gwani a Kebbi 

Sanatan Kebbi ta Kudu a Majalisar Dattawa, Garba Musa Maidoki, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC. A cikin wata wasiƙa da ya aike wa Shugaban APC na mazaɓar Rafin Zuru mai ɗauke da kwanan watan 14 ga Mayu, 2026, Sanatan ya ce ya ɗauki matakin ne sakamakon rikice-rikicen cikin gida da suka dabaibaye jam’iyyar. […]

Read more

Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi ya rasu.

Allah Ya yi wa Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Muhammad Usman Zuru, rasuwa a wani asibiti da ke ƙasar Masar, inda yake karɓar magani sakamakon fama da dogon rashin lafiya da ba a bayyana ba. Wani jami’in gwamnati a Birnin Kebbi ya ce an kai shi kasar waje domin jinya tun kafin fara azumin watan Ramadan […]

Read more

An Ceto Daliban Da Yan Bindiga Suka Sace A Kebbi

Hukumomin Najeriya sun sanar da kuɓutar da ɗaliban Sakandiren ƴan mata da ke garin Maga a jihar Kebbi su 24. Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Tinubu ya yi wa ɗaliban maraba da dawowa. Shugaba Tinibu ya kuma ya yaba wa ƙoƙorin jami’an […]

Read more

Gwamnatin Filato Ta Rufe Makarantun Jihar Saboda Tsaro

Ma’aikatar ilimi ta jihar Filato ta bayar da umarnin rufe duka makarantun jihar na furamare da sakandire sakamakon ƙaruwar matsalar satar ɗalibai a ƙasar. Hukumar Ilimi a matakin farko ta jihar, PSUBEB ta bayyana ɗaukar matakin a matsayin matakin kariya ga ɗaliban jihar. Matakin na zuwa ne bayan sace ɗaliban sakandiren Papiri a jihar Neja, […]

Read more

Matawalle Ya Isa Birnin Kebbi Bisa Umurnin Tinubu

Ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Mohammed Bello Matawalle ya isa tashar jirgin sama ta Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi, domin taimaka wa da sa ido kan yunƙurin ceton ɗaliban da aka sace a jihar ta Kebbi. A ranar alhamis ne Shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya umarce shi ya koma jihar – da ke arewa […]

Read more