Wasu mutum huɗu da ake zargi da damfarar maniyyata aikin Hajjin bana sun shiga hannu a Jihar Kebbi.
Jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta, SP Bashir Usman, ya bayyana cewa dubun waɗanda ake zargin ta cika ne bayan ƙorafe-ƙorafe daga waɗanda abin ya shafa da kuma Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kebbi suka shigar.
Sanarwar ta ce ana zargin mutanen da bayar da jakunkunan alhazai Hajji na bogi da takardun gwajin lafiya na bogi, tare da karɓar kuɗaɗe daga hannun mutane da sunan samar musu kujerun aikin Hajji.
Waɗanda ake zargin sun haɗa da Aminu Hassan Zauro, Tabiu Abubakar, Usman Attahiru, Mustapha Sani Zauro da Bello Jos.
Yan sandan sun ce babban wanda ake zargin, Hassan Zauro, ya karɓi Naira 860,000 daga hannun wani mutum da alƙawarin samar masa kujerar Hajji guda biyu.
Sanarwar ta ƙara da cewa waɗanda aka damfara sun fara zargin an damfare su ne bayan da ba su ga sunayensu cikin jerin maniyyatan da aka amince da tafiyarsu ba, duk da cewa an ba su kayayyakin zuwa aikin Hajji da ake zargin an ba su ta hanyar yaudara.
“Zauro ba shi da wata alaƙa da Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kebbi, amma ya haɗa baki da sauran waɗanda ake zargin wajen damfarar masu niyyar zuwa Hajji har ta kai ga ba su kayayyakin zuwa Hajji na bogi,” in ji sanarwar.
Rundunar ta kuma bayyana cewa har yanzu akwai wasu da ake nema ruwa a jallo, tare da tabbatar da cewa za a hukunta duk masu hannu a lamarin bayan an kama su