Sanata ya bar APC a jajibirin zaɓen fidda gwani a Kebbi 

Sanatan Kebbi ta Kudu a Majalisar Dattawa, Garba Musa Maidoki, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC.

A cikin wata wasiƙa da ya aike wa Shugaban APC na mazaɓar Rafin Zuru mai ɗauke da kwanan watan 14 ga Mayu, 2026, Sanatan ya ce ya ɗauki matakin ne sakamakon rikice-rikicen cikin gida da suka dabaibaye jam’iyyar.

Maidoki ya bayyana cewa rikicin APC ya jefa burinsa na siyasa cikin damuwa, inda ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi na yin aiki ƙarƙashinta.

Mutane a yankin Sanatan suna zargin ya fice daga APC ne saboda rashin ba shi tikitin sake shiga zaɓe a 2027.

Sanata Maidoki, yana jam’iyyar PDP lokacin da ya lashe zaɓe a 2023, daga baya ya sauya sheƙa zuwa APC.

Post masu alaƙa

Yan sandan Kano sun gaiyaci Aminu Warkal kan zargin nuna bindiga.

2027: Sama da mutum 10,000 sun nuna goyon bayansu ga Tinubu da Namadi a mazabar Limawa

Bai kamata ’yan Najeriya suke shan wahala haka ba — Atiku