Allah Ya yi wa Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Muhammad Usman Zuru, rasuwa a wani asibiti da ke ƙasar Masar, inda yake karɓar magani sakamakon fama da dogon rashin lafiya da ba a bayyana ba.
Wani jami’in gwamnati a Birnin Kebbi ya ce an kai shi kasar waje domin jinya tun kafin fara azumin watan Ramadan da ya gabata, bayan yanayin lafiyarsa ya ƙara tsananta.
Marigayin, wanda ya wakilci mazaɓar Zuru a majalisar, ana kallon sa a matsayin gogaggen ɗan majalisa kuma ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan ɓangaren majalisar dokoki a jihar.
Wani mataimaki ga gwamnan jihar kan harkokin sadarwa da dabaru, Idris Abdullahi Zuru, ya bayyana rasuwar a matsayin mai girgizawa.
Ya ce, “Rasuwar Shugaban Majalisar, Rt. Hon. Muhammad Usman Zuru, ta zo mana a matsayin babban abin kaɗuwa. Rashi ne mai raɗaɗi ba ga Jihar Kebbi kaɗai ba, har ma da ƙasa baki ɗaya.”
Ya ƙara da cewa za a bayyana ƙarin bayani nan gaba.
“Har yanzu muna tattara cikakken bayani kan yadda rasuwar tasa ta faru. Gwamnati za ta fitar da sanarwa a hukumance tare da bayyana shirye-shiryen jana’izarsa bayan tuntubar iyalansa,” in ji Idris Zuru.