labarai

Kasashen Mali, Burkina Faso, Nijar sun fice daga ECOWAS

Ƙasar Mali a maimakon ƙasashen Burkina Faso da Nijar, ta rubuta wa ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma, wato ECOWAS, takardar sanarwa na ficewa daga ƙungiyar nan take. ƙasashen sun zargi ƙungiyar da sauka daga manufofin da suka assasa kafa ƙungiyar waɗanda ke ƙunshe da aƙidar bunƙasa yankin Afirka. Sannan sun zargi ECOWAS […]

Read more

Akwai bukatar Naira Tiriliyan 1 domin ƙarasa tin Kano-Abuja

Ministan ayyuka a Najeriya, Sanata David Umahi ya ce kamfanin gine-gine na Julius Berger na neman sama da naira triliyan ɗaya domin kammala aikin babban titin Abuja zuwa Kaduna. Da yake magana a wani taro da daraktocin ma’aikatar ayyuka a Abuja, ministan ya ce farko an ware wa aikin titin Naira miliyan dubu 165 daga bisani aka ƙara kuɗin zuwa naira […]

Read more

wasu mata sun fita zanga-zangar lumana a Kano

DAGA: HASSAN ABDU MAI BULAWUS Wasu dandazon mata sun gudanar da zanga-zangar lumana a kan gadar da ke ƙofar Nassarawa domin nuna goyon bayansu ga gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, tare da yin kira ga masu ruwa da tsaki a ɓangaren shari’a kan yin adalci a hukuncin zaɓen gwamnan Kano da ake dakon jiran […]

Read more

Wani sarki ya karrama shugaban Najeriya da sarauta

  Masarautar Ukpo da ke ƙaramar hukumar Dunukofia ta bai wa shugaban ƙasa Bola Ahmad TInubu da mataimakinsa Kashim Shettima sarauta. Masarautar dai ta ba wa shugaban ƙasar nan sarautar “Eze Udo of Igbo Land”, wato “sarkin zaman lafiya na ƙasar Igbo”, sai kuma mataimakinsa wanda aka ba shi sarautar, “Enyi Ndigbo”, wato “abokin al’ummar […]

Read more

Gwamnan Jigawa ya naɗa sabon shugaban jami’ar SLU

  Gwamna Umar A. Namadi, ya amince da naɗin Farfesa Muhammad Ibrahim Yakasai, a may sabon shugaban jami’ar Sule Lamiɗo, Kafin Hausa (SLU) Wannan amincewa na ƙunshe ne a cikin jawabin da sakataren gwamnatin jihar, Malam Bala Ibrahim, ya fitar. Sannan ya yi ƙarin haske da cewa naɗin nasa ya biyo bayan miƙo sunansa da […]

Read more

Malam Aminu Kano abin tunawa ne har abada

An yi kira ga kamfani dilancin labarai na Najeriya NAN da ya dawamar da fittacen dan kishin kasa kuma dan siyasa, marigayi Malam Aminu Kano(1920-1983). Wani gogagen dan jarida kuma mai ba da shawara kan harkokin yada labarai a nan Kano, Alhaji Abdulkhadir Ahmad Ibrahim kwakwatawa ne ya yi wannan kira a cikin wata wasikar […]

Read more