Akwai bukatar Naira Tiriliyan 1 domin ƙarasa tin Kano-Abuja

Ministan ayyuka a Najeriya, Sanata David Umahi ya ce kamfanin gine-gine na Julius Berger na neman sama da naira triliyan ɗaya domin kammala aikin babban titin Abuja zuwa Kaduna.

Da yake magana a wani taro da daraktocin ma’aikatar ayyuka a Abuja, ministan ya ce farko an ware wa aikin titin Naira miliyan dubu 165 daga bisani aka ƙara kuɗin zuwa naira miliyan dubu 654.

Sai dai ya ce a yanzu gwamnati ba ta da shirin biyan sabon farashin da kamfanin ya nema saboda rashin kuɗi.

Majiyarmu ta ruwaito cewa an ba da kwangilar aikin ne tun a shekarar 2017 amma ba a fara ba sai a shekarar 2018, kuma tun shekarar 2021 ya kamata a kammala titin wanda ɗaya ne daga cikin manyan ayyukan gwamnatin Buhari.

Sai dai hakan bai samu ba har gwamnatin ta sauka a shekarra 2023 duk da cewa rahotanni sun tabbatar da cewa yanzu haka an kammala fiye da rabin aikin titin.

Post masu alaƙa

Jigawa Za Ta Bai Wa Alhazai Abinci Sau Uku a Rana a Hajjin 2026

Namadi Ya Kaddamar da Shirin Fadada Ilimi yayin da SLU ta Yaye Dalibai Sama da 4,000

Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Jigawa Ta Taya Gwamna Namadi Da Musulmi Murnar Eid-el-Fitr