Da buƙatar samar da takin zamani ga manoman Najeriya – MDD

Mataimakiyar sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Amina Muhammed ta nemi gwamnatin Najeriya ta samar da sabbin tare-tsare da za su baiwa manoman ƙasar damar samun takin zamani.

Amina ta bayyana haka ne yayin tattaunawarta da jaridar TheCable da ke Najeriya, a birnin Washignton DC na Amurka, yayin da aka mata tambaya kan yadda za a bunkasa samar da abinci a Najeriya.

“Yadda Najeriya ke fitar da takinta na taimakawa wajen habbaka tattalin arzikinta sai dai kuma manoma a cikin gida ba sa iya saya saboda tsada”, in ji Amina.

Ta kuma bayar da shawarar gwamnati ya kamata ta haɗa hannu da masu masana’antu na cikin gida domin samar da takin ga manoman da ke cikin gida.

Post masu alaƙa

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC

Ƴansanda sun ƙara tsaurara matakan tsaro a bikin Takutaha, tare da gargaɗin masu yunkurin tada zaune tsaye.