Yan bindiga sun lafta wa manoma sabbin haraji a Sakkwato

Mazauna akalla ƙauyuka 26 a Ƙaramar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato sun fara tara kuɗi domin biyan sabon harajin da ‘yan bindiga suka ƙaƙaba musu kafin noma gonakinsu a daminar bana.

Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa ’yan ta’addan sun yi barazanar yin garkuwa ko halaka duk wanda suka gani yana aikin gona kafin cikar wa’adin, a daidai lokacin da ake shirin fara ayyukan noma na damina.

Sun ƙara da cewa, ƙungiyoyin ‘yan bindigar sun ba su wa’adin kwana uku, tare da gargaɗin cewa manoma kada su kuskura su shiga gonakinsu har sai an biya kuɗaɗen harajin da aka ɗora wa ƙauyukan da abin ya shafa.

Ƙauyukan da lamarin ya shafa sun haɗa da Garin Faji, Cina Barka, Zululu, Dan Gari, Garin Maigayya, Gardi, Katsira, Garin Baushe, Sulmawa, Zakin Ganga, Dan Kware, Garje, Dogon Faru, Son Allah, Garin Galadima, Kafchi, Matabaya, Garin Labo, Zango, Kaifin Aska, Tsauna Dogo, Tudun Wada, Rambadawa, Ga Itace, Nasarawa da kuma Garin Idi.

Wani mazaunin yankin  ya ce ’yan bindigar ya ce, “’Yan bindigar sun ba al’ummomin wa’adin kwana uku, suna masu cewa babu wanda zai je gona har sai an biya kuɗin. Duk wanda aka kama yana noma za a kashe shi ko kuma a sace shi, kuma ba za a sako shi ba sai an biya kuɗin fansa na Naira 500,000.”

Ya ƙara da cewa mazauna yankin sun riga sun fara tara kuɗaɗe domin cika buƙatun ’yan bindigar.

Wani mazaunin ƙauyen Zululu, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce yana shirin zuwa gonarsa aranar Juma’a ne lokacin da ya samu labarin wannan lamari.

Ya ce, “An sanar da mu cewa ’yan bindigar sun dakatar da ayyukan noma na tsawon kwana uku har sai ƙauyukan sun biya harajin da suke karɓa a kowace shekara.

“Sun ce da sun so bari mutane su je gonakinsu sannan su kashe wasu su kuma yi garkuwa da wasu, amma sun fi son a ba su kuɗi. A cewarsu, jami’an tsaro suna kwace musu dabbobinsu, don haka ba za a yi noma ba har sai an biya harajin.”

Ya ce ana sa ran sarakunan gargajiya da malamai daga ƙauyukan da abin ya shafa za su gana da ’yan bindigar domin tantance adadin kuɗin da kowace al’umma za ta biya kafin a ci gaba da noma.

A cewarsa, shekaru da dama ke nan ’yan bindiga suna tilasta wa al’ummomin yankin irin waɗannan biyan kuɗaɗe.

Ya ce, “Muna biyan kuɗi kafin shuka, sannan wani lokaci bayan duk wata biyu ko uku. Ko mun biya yanzu, za su iya dawowa bayan wata uku su ce ba za a girbe gero ba har sai an sake biyan wani haraji.

“Tsakanin Naira miliyan huɗu zuwa miliyan shida sune karɓa daga kowace al’umma. Mazauna ƙauyuka na bayar da gudunmawa gwargwadon ƙarfinsu. Wasu gidaje na bayar da Naira 1,500 ko 2,000, yayin da a wasu ƙauyukan manoma ke bayar da har Naira 5,000 kowannensu, gwargwadon yawan al’ummar ƙauyen.”

Post masu alaƙa

Zulum ya bai wa sojoji kyautar motocin yaƙi, ya tallafa wa ’yan gudun hijira

Wasu Tsiraru Ne Ke Rura Matsalar Tsaro A Najeriya — Christopher Musa

Rundunar tsaron Nijeriya ta bayyana damuwa kan mutuwar Janar Rabe a hannun ƴan bindiga