Soji

An kashe fiye da ƴan bindiga 200 a jihar Kogi

Hukumomin Najeriya sun ce jami’an tsaro sun kashe fiye da ‘yanbindiga 200 a wani “gaggarumin samamen hadin gwiwa” da aka gudanar a jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya, yayin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke ci gaba da ƙoƙarin daƙile matsalar rashin tsaro a ƙasar. ‘Yansanda sun kuma kama wasu da ba a fayyace adadinsu […]

Read more

Sojoji sun ceto Kansila da malami da aka sace a Borno

Sojojin Najeriya a ƙarkashin Operation Hadin Kai sun ceto fararen hula biyu da ‘yan ta’adda suka sace a kan hanyar Buni Gari-Buratai da ke Borno, bayan wani aikin bincike da ceto cikin gaggawa da ake gudanarwa. Majiyoyi sun shaida cewa, sojojin rundunar 27 Task Force Brigade tare da haɗin gwiwar rundunar 135 Special Forces Battalion […]

Read more

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta yaye ƙarin kurata 3,439

Hafsan sojin ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu (NAM), ya yi kira ga sabbin jami’an soja 3,439 da aka horas da su dukufa wurin nuna ƙwarewa yayin gudanar da ayyukansu. Dakarun da aka ɗauka waɗanda ke cikin runduna ta 89 na rundunar sojojin Najeriya, sun samu nasarar kammala horon na tsawon watanni shida a […]

Read more

Majalisa ta buƙaci Tinubu ya ɗauki sabbin sojoji 100,000

Majalisar Dattawan Najeriya ta buƙaci Tinubu ya umarci rundunonin sojin ƙasar su ɗauki ƙairin jami’an aƙalla 100,000 domin ƙarfafa yaƙin da gwamnati ke yi da matalar tsaro a ƙasar. Matakin na zuwa ne bayan da ɗan majalisar dattawa daga jihar Kebbi, Yahaya Abdullahi ya gabatar da ƙudiri kan batun, inda ya alaƙanta hakan da sace […]

Read more

Sojojin Najeriya Sun Halaka Yan Fashin Daji A Zamfara

Rundunar sojan sama ta Najeriya ta ce ta yi nasarar kashe ‘yanfashi da dama waɗanda ba ta faɗi adadinsu ba a garin Tsafe na jihar Zamfara bayan wani hari ta sama. Mai magana da yawun rundunar,,Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce an kai hare-haren ne kan sansanin ‘yanfashi na Sauri ranar Juma’a bayan tattara bayanan […]

Read more